SCHIZOPHRENIA DA LARURAR GANE-GANE (WADANDA ALJANU SUKE BUDEWA IDO)

 Tun lokacin da na kalli wani wasan kwaikwayo da ake cewa Beautiful minds, wanda ya bi diddigin faman da wani masanin lissafi da ake cewa John Nash yayi da schizophrenia, hankali na ya karkata ga tunanin mecece wannan schizophrenia? 

John Nash dan baiwa ne a fannin lissafi. Daga cikin irin gudunmawarsa da ba za a iya mantawa ba a lissafi ,John ya taimaka wajen yiwa mahangar Adam Smith kwaskwarima a fannin ilimin tattalin arziki, wannan aiki da John yayi ya taimaka wajen canja yadda ake koyar da ilimin tattalin arziki a duniya. A hakikanin gaskiya, wannan daya ne daga cikin gudummawoyi masu dimbin yawa da John ya samar a fannin lissafi.

Saidai akwai abinda yake damun John, wata cuta da ake cewa Schizophrenia. Ko a cikin wannan wasan kwaikwayo, anyi tariya akan rayuwar da John yayi da abokin kwanansa a jami'a. Wannan abokin kwana na John shine babban abokinsa kuma abokin tattaunawarsa a fannoni daban daban da suka shafi akida, siyasa, soyayya da sauransu. Wannan abokin na John har wata 'ya gare shi wadda yake zuwa da ita daga lokaci zuwa lokaci kuma John ya san ta itama ta san shi. John ya sha fama da gujewa hukumar sojojin Rasha don gujewa wani aiki da suke nemansa yayi musu wanda zai taimaka wajen daukaka karfin tasirin Tarayyar Soviet a wannan lokaci. Akwai ma wani lokaci da suka dauke shi suka kai shi wata ma'aikata don yin wannan aiki. Saidai tun daga kan wannan abokin kwana, da wannan yarinya da abokin John yake Baffa a gareta da mu'amalarsa da mutanen rasha, duk a kwakwalwar John kawai suke faruwa, kuma shi John bai san ba na zahiri bane. John bai fara sanin bashi da lafiya ba sai da yayi aure, matarsa ce ta fara fahimtar akwai matsala a tare da shi.

Kodayake daga baya John yayi yaki da zuciyarsa don ganin ya yaki irin wadannan gane gane, amma fa bai daina ganinsu ba, saidai kawai, ya fahimci wadannan mutane da abubuwan da suke faruwa ba na gaske bane kuma yayi musu mazauni daidai dasu.

Wannan shine abinda ya wakana da John, amma menene schizophrenia a mahangar likitocin zamani. Cutar schizophrenia dai ita ce irin wadda John yayi ta fama da shi. Mutum yana iya rayuwa bisa doron wata zahiriyya da ba kowa yake cikinta ba. Bayan mutanen da mai jinyar ya sani na zahiri, akwai wasu mutanen ko halittu ko wurare da yake mu'amala da su da ba kowa yake ganinsu ba. Wannan larura ta sanya likitocin zamani a ruɗani, don har kawo yanzu ana cewa ba a fahimci cutar ba. Akwai gwaje gwajen ƙwaƙwalwa da ake yi ga masu jinyar a kullum, kuma abin alajabin yana ƙara yawa ta hanyar ganin alamomi da suke nuna cewa wasu alamura na daban suna mamayar wani sashe na kwakwalwa wanda a zahiri babu su. Hakanan ana lura da wani irin yanayi da nufashin mai jinyar yake shiga idan abin ya motsa masa.

Bayan John Nash, akwai shahararrun mutane irinsu; Haruna Rashid, Zelda Fitzgerald (Matar marubucin labaran almara F. Scott Fitzgerald), Eduard Einstein ( Dan autan Albert Einstein). Wasu ma sunce a karshen rayuwar Isaac Newton, ya yi fama da larurar. 

MAHANGAR LIKITOCIN ZAMANI

Babu wani cikakken bayani bayan hasashe da shaci fadi akan abinda ke jawo wannan larura a mahangar zamani. Daga cikin irin shaci fadin akwai wani jan hankali da wani yake cewa tsananin yunwa lokacin da mace take dauke da ciki na iya tasiri akan yaron da zata haifa ta hanyar zuwan jaririn duniya da wannan cutar.

Likitocin zamani sun dauka wannan cuta irin sauran cutuka ne na ƙwaƙwalwa, kawai dai ilimi ya gaza yin bayani akan wasu abubuwa da suke faruwa da majinyatan. Misali, mutumin da yake cikin wani kauye da bai san ta inda zai bar kauyen ba a Kano ya rika baka labarin wata unguwa a China da kuma mutanen da suke zaune a unguwar, kuma daga karshe sai a tabbatar da hakan. Wannan ya ci karo da duk wani abu da aka gina likitancin zamani a kai, tun kawo daga gundarin tubalin ginin aikin likitancin zamani, wato kimiyya zuwa zallan ilimin a matakin kwarewa. Sa'annan akwai wadanda suka yarda cewa ana daukar irin wannan jinya ne ta jikin kwayoyin gado (DNA) shi ma ba a tabbatar ba saboda babu wani bincike da zai iya bayyana hakan ta amfani da yare da hanyoyin da kimiyya ta shimfiɗa.

MAGANIN SCHIZOPHRENIA A MAHANGAR LIKITANCIN ZAMANI

Ana amfani da makamanciyar hanyar magance Multiple Personality Disorder wajen magance matsalar Schizophrenia. Amfani da mutanen da suka kware wajen fahimtar yadda kurwa take aiki yana daga cikin hanyoyin da likitoci suke amfani da shi wajen magance irin wannan matsalar. Kodayake ba lallai ne ni na iya sanin dukkan hanyoyin da likitocin zamani suke bi wajen tafiyar da masu fama da wannan larura ba, amma zan iya cewa har yanzu babu wata hanya ta garanti da ake magance ta.

MASU GANE GANE KO WADANDA ALJANU SUKA BUDE WA IDO

A al'ummar mu, ana samun wasu mutane da suke da baiwar ganin abinda ba kowa ne yake iya gani ba, wasu suna iya jin magana, mai ma'ana da tushe wadda ba wanda yake jinta a lokacin. Hakanan wasu suna tsintar kansu a wasu wurare da a zahiri basu je ba. 

Na taba duba wata yarinya da take fama da wannan matsalar, tana da ƙawa Fatima sunan mijin kawar Sarkin dawa Ali. Yarinyar ta ce min tana da alaƙa ta kusa kusa da Fatima, wani lokaci suyi faɗa wani lokaci su saɓa. Idan an bata wa yarinyar rai itama kawar tana jin haushi. Fatima tana iya fada wa yarinyar boyayyun al'amura game da wadanda take rayuwa tare da su.

Hakanan akwai wani yaro da yake kawowa mahaifina turare, shi kwanan nan ne san shi, yaron yana iya ganin mutanen boye da suke tafe da mutum, zai iya fada maka abinda tabbas hakane ba shakka akanka kuma kaima ka sani.

RAAYIN BAHAUSHE GAME DA MASU GANE GANE

A zahirin gaskiya bahaushe bai dauki masu gane-gane a matsayin marasa lafiya ba, hasali ma, Hausawa suna daukar abin a matsayin wata baiwa ce daga Allah, kuma akan yi amfani da ita wajen bada magani ainun. Wasu kuma suna amfani da ita wajen tara ilimi matuƙa da dai sauransu.

Dalilin da yasa bahaushe bai dauki masu gane gane a matsayin marasa lafiya ba shine, bahaushe ya yarda da Aljanu, kuma ya yarda Aljanu suna budewa wanda suke so ido don suyi mu'amala da shi. Idan ka dan yi nutso cikin ilimin bori, wanda yake daya daga cikin sahihan hanyoyin likitanci a wajen bahaushe, kuma tushen fahimtar bahaushe dangane da Aljanu, zamu ga cewa bahaushe ya karkasa Aljanu gida gida, kuma kowacce zuri'a ta ɗan adam akwai aljani ko aljanun da suke gada. Misali, ni a matsayina na mafarauci, zuri'a ta tana gidan Fulani; dangin Mafarauta. Saboda haka, a cikin zuri'a ta, za a iya samun wanda Aljanu suka bude wa Ido, idan sun bude masa ido to zasuyi mu'amala da shi, to a nan zasu sanar da shi maganin gida da na jeji saboda su aljanun jeji da magani aka san su. Daga cikin manyan aljanun da suke gidan Fulani akwai Maidawa, akwai Inna, akwai Mai gizo da sauransu. Kowanne a cikinsu akwai halinsa, da irin shigarsa, da irin abubuwan da yake so da wadanda baya so. Hakanan wadanda suke mu'amala da shi, zasu rika ganinsa ne a wannan siffa, wani lokacin ana samun canji a siffar da suke dauka amma dole zasu bar shaidar cewa su ne su wane. Hakanan idan gidan malamai ne, akwai Malam Alhaji, wanda idan ya so mutum yake sa shi gane karatu da sauki, yake kuma bashi taimako irin na malamai don sauran mutane su amfana, shima yana da nasa siffofin (ina jin farin kaya yake sawa), da abubuwan da yake so, da wadanda baya so da sauransu. Karin aljanun da Hausawa suka yarda da su kuma suke mu'amala da su akwai arne, barhaza, kuturu, Sarkin Fulani, Sarkin aljanu Sulaimanu, danko, dan galadima, barade, arziki, duna, kure,  magajiyar jangere, Sarkin aljanu biddarene, kwakiya, Sarkin aljanu shekaratafe, Sarkin aljanu zurkalene, Sarkin rafi, Sarkin gwari, Sarkin wanzamai, da dai sauransu.

Ba zaka fahimci larurar buɗar ido ba a al'adar Hausa har sai ka fahimci dabi'un aljanu da Hausawa suke amfani da su, don ta haka ne za a iya gane wanne aljani ne yake tare da mutum har kuma a fahimci irin mu'amalar da yake so suyi. Kuma ta haka ne ake iya gyara aljanin da yake tare da mutum ta yadda ba zai cutar da shi ba.

Shi aljani kamar saitin waya ne, kowanne aljani zai iya zama a kan mutum duk irin karfinsa, amma matsalar shine dole sai dai idan da aljanin da wanda aljanin yake tare da shi suna kan saiti. Kamar ka kamo tashar rediyo ne, idan an dace, an hau kan mitar daidai sai a ji sauti in ba a dace ba sai a ji ƙugi.

Kamar yadda na fada a baya, ana iya samun aljanun da suka budewa mutum ido suna cutar da shi, ko mutum ya fita daga hayyacinsa, idan aka samu irin wannan matsalar to shine maganar magani ta shigo ciki. Amma maganin da aka fi yi shine wanda za ace a gyara kurwar mara lafiyan don ya wanye lafiya a lokacin mu'amalarsa da aljanun. Wannan ita ce hanya mafi sauki da ake iya bi wajen magance matsalar.

Kodayake akwai malamai masu yin rukiyya ga mutane masu irin wadannan matsaloli, amma tasirin ruƙiyya yana raguwa ainun a wanna zamani. Dalilin da yasa haka shine, masu rikiyyar suna fama da kalubale daban daban a lokacin da suke yin rukiyyar, ga wuya ga rashin biyan bukata ga kuma tsananin barazana ga ahalin shi mai ruƙiyyar.

SHARHI

Idan muka lura zamu ga cewa, cutar schizophrenia da kuma Budar Idon Aljanu suna matukar kamanceceniya wasu ma zasu iya cewa abu daya ne. Nima ina kan ra'ayin cewa Schizophrenia da budar idon Aljanu abu guda ne.

Hakanan babban abin ban sha'awa akan wannan larura shine, su likitocin zamani sun yarda cewa bata da magani, su kuma likitocin gargajiya basu dauke ta a matsayin cuta ba, a inda ta zama cuta kuma suma basu dogara akan maganinta ba, saidai yadda za a shawo kan mai ita. 

Dadin dadawa, likitocin zamani sun yi wani hasashe cewa yunwa a jikin mace mai ciki tana da tasiri wajen samar da yara masu fama da schizophrenia, a al'adance kuma, rashin abinci wani mataki ne da wadanda ma basu da baiwar gane gane suke bi wajen fadawa cikin yanayin gane gane don biyan wasu bukatunsu, duk da dai wasu suna amfani da itatuwa masu jefa ruhi cikin yanayin maye, kamar irinsu tabar wiwi, kashin kadangare, giya, zakami da sauransu amma hakan bai kawar da da'awar cewa yunwa ma tana daga cikin hanyoyin da ake bi ba. Bayanin yadda ake bi wajen cimma wannan muradin ya wuce gejin da aka tsara littafin nan akai.

Abin lura ne cewa bahaushe yayi matukar kokari wajen ganin al'adar sa bata bada kofa gane gane ya zama cuta da zata tada hankalin mai yi ba. A cikin hikima al'adar bahaushe tayi nasarar rinjayar mutane cewa gane gane ba cuta bace baiwa ce, kuma mutane da yawa suna fama da yawan gane gane, amma da yawa basa faɗa, sun rike shi a matsayin wata baiwa da Allah ya hore musu kuma suke amfani da ita ko ta hanyar da ya dace ko ta hanyar da bai dace ba. Wannan ba karamar nasara bace ga al'adar bahaushe, don kuwa wannan rinjaye da aka samu shine babban fafutukar da masana kimiyya suke wajen ganin sun magance cutar. Kuma mafi tasirin hanyar da likitocin zamani suke bi wajen bi da cutar shine psychotherapy. Psychotherapy din da al'adar Hausa ta samar yana daga cikin kololuwar nasara a cikin hanyoyin magance matsalar gane gane ko jiye jiye da kimiyya take muradin kaiwa. Za a iya cewa, al'adar bahaushe ta zo da magani kyauta ga masu gane gane ko jiye jiye.

Ba iya hausawa ne sukayi amanna cewa gane gane ba cuta bane baiwa ce, yawancin al'adu na gargajiya akan haka suka ginu.

Ina fatan wannan rubutu zai zama iya ruwa fidda kai ga wanda bai yarda cewa aljanu suna da alaka da gane-gane ba, ta hanyar fahimtar cewa ko menene yardar ka, Indai zaka yi amfani da darasin da ke cikin wannan rubutu.

Sanin kanka da sanin abubuwan da kake gani sun isa fidda kai daga cikin duk wata fargaba da wannan yanayi ka iya jefa ka ciki.


Mujahid Khalid,

Garkuwan Dawan Rano,

12/05/2023

Comments

Popular posts from this blog

A Way to Burum burum

Tsokaci da shawarwari ga masu matsalar shafar Aljanu a mahangar al'ada ko likitancin zamani