Tsokaci da shawarwari ga masu matsalar shafar Aljanu a mahangar al'ada ko likitancin zamani
Gabatarwa
A al'ada ta Hausawa, ana samun mutane masu larurar shafar aljanu, mutanen da aljanu suke sanyawa su fita daga ainihin hayyacinsu su shiga wani yanayi daban. Irin wadannan mutane suna sauya ɗabi'arsu da aka sansu da ita zuwa wata ɗabi'a daban. Misali, mutumin da bai jin turanci sai ya canza yare yana turanci kamar Bature, ko mai kunya ya koma mara kunya da sauransu.
Irin wannan larura tana iya jawo matsaloli marasa adadi. Wasu daga cikin matsalolin suna canjawa daga lokaci zuwa lokaci, wasu kuma suna zaune a yanda suke. Baya ga sauyin dabi'a da majinyaci yake samu idan hakan ya faru da shi, ana iya samun wasu jinyoyi na zahiri da suke mamayar majinyacin a matsayin yan rakiya. Wadanna jinyoyi da suke zama yan rakiya, suna iya faruwa kafin majinyanci ya tsinci kansa a wannan yanayi ko bayan ya dawo hayyacinsa, misali, ciwon kirji, gazawar zuciya, ciwon ciki, ciwon mara, ciwon kai, ciwon kafa ko ciwon jiki gabadaya ka iya bijirowa a duk lokacin da alamomin babbar jinyar suka fara bayyana ko bayan sun bayyana. Hakanan, akwai bayyanar wani kumburi a wani sashi na jiki misali maruru, kakuluwa, janbaɗe da sauran nau'ika na ƙurar a lokacin da kunyar ta bakunci mai ita, ko bayan ta tafi.
Majinyaci da yake fama da larurar Shafar Aljanu yana iya rasa hankalin da zai iya tuna me ya faru da shi a lokacin da wannan larura ta bijiro masa.
A likitancin zamani, wannan larurar tana daukar sunan Multiple Personality Disorder ko kuma Dissociative Identity Disorder. Likitoci sun ce mutum yana samun kansa a wani yanayi da yakan iya canja dabi'unsa na yau da gobe zuwa wasu baƙin ɗabi'u waɗanda suka bambanta da wadanda aka sani. Wadannan dabiu dake bijirowa akan mutum sukan fara daga biyu zuwa sama.
Tsokaci
Duk da yake na sani cewa za a samu wadanda suke da ja akan ra'ayina, ni kam fahimta ta ta tsaya ne akan cewa Shafar Aljanu da Multiple Personality Disorder Abu ɗaya ne. Kodayake yawancin aikin likitancin zamani anyi shi ne ba tare da tasirantuwar al'ada ko addini ko camfi ba, amma hakan ba yana nufin akwai wasu sababbin cutuka da aka kirkiro domin likitancin zamani ba. A saboda haka, cutuka da larurorin da aka sani tun na Dauri (na zamanin da), sune dai a wannan lokaci da ilimin boko yake sharafi. Kodayake, za a iya samun sauyi wajen samar da sababbin hanyoyin da ake bi wajen warkar da wannan larura ta bangaren likitanci na zamani, to amma har yanzu ruwa yana maganin dauɗa, ma'ana, har yanzu hanyoyin waraka na gargajiya suna tasiri, hasali ma, a al'ada ta mutanen mu, har yanzu ita ce akan gaba idan an lura cewa mutum ya kamu da cutar shafar Aljanu ce. Bisa shimfiɗa wadannan dalilai ne, don na saukakawa kaina da kuma mai karatu, na yanke shawarar daukar Multiple Personality Disorder da Larurar Shafar Aljanu a matsayin abu ɗaya.
Sababin Samuwar Larurar Shafar Aljanu (MPD) a mahangar likitancin gargajiya.
A mahangar likitancin na gargajiya, suna ganin cewa shafar aljanu ne sababin larurar Shafar Aljanu (MPD). Wadannan aljanu suna iya zama baƙi, wadanda mai larura yayi kicibis da su a sakamakon wani tsautsayi ko kuma wadanda ya gamu da su da saninsa don biyawa kansa wata bukata. Hakanan, wadannan aljanu suna iya kasancewa na gado, wato waɗanda majinyacin ya gada daga iyaye da kakanni. Hakanan sukan iya zama wadanda aka yi masa ture ta hanyar sihiri ko maita.
Sababin Samuwar Larurar Shafar Aljanu (MPD) a mahangar likitancin zamani.
Babu wani takamaiman dalili da yake zama silar samuwar wannan yanayi na shafar Aljanu (MPD) a mahangar likitancin zamani, saidai wasu suna cewa yana samo asali ne daga dalilin cin zarafi ko tsananin firgici da yaro yake shiga a cikin kuruciyarsa, wannan ya haɗa da tsananin bakin ciki sakamakon tsangwama, fyade, cin zali, bautarwa, tsoratarwa da sauran irin wadannan aikace aikace. A duk lokacin da yaro ya tsinci kansa a yanayi irin wannan, to yanayin ka iya zama silar tsintar kansa a wannan larura ta Shafar Aljanu (Multiple Personality disorder).
Hanyoyin da likitocin gargajiya ke bi wajen magance Larurar Shafar Aljanu (MPD)
A fahimta ta gargajiya, ana iya warkewa tsaf daga yanayin shafar aljannu wanda ka iya jawo canjin halayyar ko dabi'a. Akwai hanyoyi da yawa da masu magani mabambanta suke amfani da su don ganin sun magance irin wadannan matsaloli.
Misali, yan bori suna amfani da kiranyen aljanu da suke kan majinyacin (wadanda suke zuwa bakunci), suyi magana da su, su kuma su fadi me za ayi musu sai su tafi. Yan rukiyya suna amfani da ayoyin Alkur'ani masu zafi don azabtar da wadannan aljannu har sai sun tankwara su suyi abinda aka umarce su. Maharba, mafarauta da wanzamai suna amfani saiwoyi, da garin burgi da hayaƙi da sassake sassake da sauransu wajen ceto kurwar majinyacin daga hannun aljannun da suke hawa kan masu larurar. Haka kuma akwai malaman da suke amfani da hatimi, ƙo ayoyin Kur'ani da tawaida da barori wajen hada rubutun sha, ko laya ko guru ko kambu da sauransu wajen magance matsaloli irin wannan yanayi. Wadannan ba Dukkanin hanyoyin da masu magani a gargajiyance suke amfani da su bane, misalai ne.
Hanyoyin da likitocin zamani ke bi wajen magance Larurar Shafar Aljanu (MPD)
Babu wani takamaiman maganin wannan larura a mahangar likitancin zamani. Amma ana iya dora majinyacin a kan wasu hanyoyi da zai iya rayuwa da cutar ba tare da ta rage shi ga wajen mu'amala da kuma cimma muradun rayuwarsa ba. Daga cikin irin shawarwarin, likitocin zamani sun bada shawarar kada a dora mutum kan wani tsari na magance wannan dabi'a har sai ya mallaki hankalin kansa, saboda sun lura cewa yawanci majinyatan suna fama da larurar rashin mai da hankali akan abinda ke gabansu idan suna kan kuruciyarsu. A saboda haka, dora su akan shawarwari da tsarin shan magani yana wahala. Hakanan akwai wasu abubuwan da likitocin suka wassafa wadanda zasu taimakawa mara lafiyan wajen ganin ya wanye lafiya a irin wannan yanayi da kan iya bakuntarsa. Magungunan da ake bawa mutane masu matsalar ƙwaƙwalwa don su kashe musu jiki da rage aikace aikacen kwakwalwa suna taimakawa majinyacin. Amma psychotherapy (tattaunawar gani da ido tsakanin majinyaci da masanin matsalolin ɗabi'a) suna daga cikin hanyoyin da ake bi-da irin wannan cuta a zamanance.
Shawarwari ga masu matsalar shafar Aljanu (MPD)
Na san ya zuwa yanzu, mai karatu ya fara tunanin wacce hanya ce ta fi tasiri wajen magance wannan larura musamman kasancewar an kawo ra'ayoyi mabanbanta daga bangarori biyu da muke tattaunawa a kai, wato likitancin zamani da na gargajiya. To amma mafi gamsarwar batu shine shawara ta rage ga mai shiga rijiya, wato shi majinyacin ko masu alhakin kula da shi.
Wadannan shawarwari kuwa da zan bayar a kasa zasu amfani majinyaci ba tare da la'akari da hanyar da ya bi wajen neman magani ba.
1. Idan majinyacin yana da ciwon gyambon ciki, a tabbatar an tanadi kyakkyawan maganin wannan ciwo wanda aka san yana da tasiri a kan majinyacin. Sarkewar numfashi da hauhawar bugun zuciya su ne matakai na farko da majinyanci zai iya tsintar kansa idan zai fita daga hayyacinsa, wadanda su kuma suke taimakawa wajen tashin ciwon ulcer da gaggawa.
2. Ga masu matsalar cutukan kirji, yana da kyau a tabbatar da maganinsu a kusa da su (na gargajiya ko na zamani, ya danganta da wanda ka zaba), domin sauyin bugun zuciya da sarkewar numfashi ka iya jawo ciwo mai radadi ga kirji.
3. Ga masu matsalar ciwon mara, yana da kyau a tabbatar akwai maganinsa a kusa don hakan yana iya motsa wannan ciwo na mara.
4. Yana da kyau a guji bata wa majinyanci rai, ko, ko firgita shi ko kuma barin shi a muhalli mai yawan hayaniya ko muhallin da ƙara tayi yawa.
5. A kula da yanayin abincin da bai karbe shi ba, kar a bashi.
6. Wannan ciwo na shafar aljannu yana iya jawo kumburin ciki, fuska, kafafuwa da hannaye, saboda haka a tabbatar zuciyar majinyanci tana aiki a cikin koshin lafiya a kodayaushe don gujewa wadannan kumburi, akwai magunguna a gargajiyance (ban san na likitancin zamani ba) wadanda suke kara karfin zuciya matuka.
7. A rika samar da magunguna da zasu karfafa garkuwar jikin majinyacin (antibiotics a zamanance) ko wasu nau'ika na birgi da suke aiki kwatankwacin iri ɗaya.
8. Ayyukan ibada (daidai da addininka) suna taimakawa majinyaci wajen raguwar yawan tashin wannan larura.
9. A guji amfani da maganin kashe zugi ko wanne iri ne (gargajiya ko na asibiti), don majinyacin yana samun kansa a yanayin ciwon jiki mai tsanani bayan ya dawo hayyacinsa. Yawan amfani da maganin kashe zugi ka iya jawowa majinyaci wasu baƙin cutuka da kuma sanya shi ya dogara kacokan da wadannan magunguna ko da jinyar ko babu.
10. A nazarci turarurrukan da majinyacin baya so sai a guji amfani da su a inda yake. Sannan a rika amfani da wadanda suke sanya zuciyarsa cikin kwanciyar hankali. Wannan ya fi tasiri idan an dauki hanyar warkarwa ta gargajiya
12. Majinyanci ya yawaita yin sadaka musamman ga ƙananan yara. Ko kyauta daidai gwargwadon iyawarsa ko wani aiki na taimako, domin shi aikin taimako yana kwantar da hankali kuma yana ƙara nutsuwa a jikin dan adam.
13. A kula da irin mutanen da majinyanci zai yi mu'amala da su.
Tare da wadannan shawarwari, yana da muhimmanci a nemi taimako na dindindin ga majinyanci, ko na gargajiya ko na zamani, sannan a tsaya akan mai magani guda ɗaya tai a lokaci ɗaya, a yi hakuri da sanin cewa waraka tana wajen Ubangiji. Yana da kyau a guji mu'amala da masu maganin da ba a aminta da sanin aikinsu ba.
Haka kuma, amfanin wadannan shawarwari da na lissafo a sama shine don su taimaka wajen saukakawa majinyacin kafin a fara yi masa magani ko a lokacin da ake masa magani, tunda shi magani ba a san ranar da za a warke ba.
Mujahid Khalid
Garkuwan Dawan Rano
06/04/2023
Comments
Post a Comment