SHAWARWARI GA MASU DEPRESSION
Ko ƙarya ce in ka bata gaskiya watarana sai ta baka. Idan kana biɗar wani abu kar ka fasa. Idan masoyiya ce take biɗar masoyi, kar ta fasa, watarana zata samu abinda take so matukar ta bada gaskiya da amana ga abinda take. Na ga amfanin naci a gurare da yawa. Naga darasi akan mutane da dama.
Lokacin da na fara harkar mu ta gado (harkar jeji), ranar farko da na shirya nace zan tafi farauta akwai wanda yace indai na iya zuwa ba zan iya dawowa ba. Na ɗauki gorar da kaka na yake riƙewa, nayi tafiyata. Haka muka je lafiya muka dawo lafiya.
Idan na fito cikin unguwa, mutane suna kallona suna cewa 'Alabuda, alabuda, cau, cau, cau' da izgilanci. 🙂 Suna ganin wancan da yayi rayuwarsa a birni, dan boko, da girmansa yace zai yi farauta. Wasu suce shirme nake, zan daina, wasu su ce zan shiga hankali na gashinan dai.
Amma da na bawa abin gaskiya, kuma na rike abinda nake da gaskiya da amana, sai Allah yasa min albarka a ciki.
Ina iya tuna watarana ana wasan maƙera, sai nazo ina recording video, saboda abin ya bani sha'awa, kawai sai wani ya ce a canja kiɗan a maida shi kiɗan farauta (kowanne bangare suna da irin kidansu da yake zama tambarinsu), kuma haka akayi, amma kuma sai na amsa kiran. Wasu mutanen suka ce ya akayi haka ta faru? Nace GADO GIRMAN ƊA, KOWA YA RAINA GADO BA NASHI BANE.
Daganan masu yimin kirari da izgili suka fara sunkuyar da kai ƙasa, masu cewa karya ne suka fara ɗaukan darasi na rayuwa.
A hankali a hankali, ba tare da girman kai ba, abinda ban sani ba in tambaya, abinda na sani in kara sani, Allah ya cigaba da hada ni da mutanen kirki, wasu sa'o'i na ne, wasu sun girme ni wasu na girme su, har Allah ya tara min sani mai yawan gaske a dan kankanin lokaci bayan ya warkar dani akan ciwon da yafi damu na. Yanzu haka saidai ince Alhamdulillah.
Mutane da yawa sun sha tambaya, wai meyake damu na? Wasu a baya ma suna tunanin anya ba na ɗauki hanyar rasa hankali na ba?
Wasu suna ta magana ta a bayan ido na, suna cewa yakamata ayi wani abu a kaina, saboda ya za ayi mutuminda yasan computer, daya daga cikin jiga jigan organizers na Google Developer Festival Na farko a Kano, mutum me skills daban daban a computer, da degree a mathematics da certifications masu dimbin yawa a fannonin computer, amma duk ya watsar yake wannan harka?
A lokacin ina jin haushi wadannan tambayoyi, don bani da amsarsu. Kuma nima neman amsar nake, saidai ina iya haɗiyewa domin na ji a jikina akwai manufa.
A hakan na cigaba da yi, tare da kalubale da nake fuskanta na sauyin muhalli, da dabi'a, da al'adu har na fara samun kaina. Amma ni shaida ne cewa ba abu ne mai sauki ba, kuma ga duk wanda ya samu kansa a irin yanayin da na samu kaina, to sai an daure.
Amma dunkulin amsar tambayoyin jama'a, akan dalilin canji da na samu na rayuwa, wannan kuwa haka Allah yaso. Na tsinci kaina a yanayi na abinda ake cewa depression, kuma ta hanyar nutso cikin asalin nasaba ta Allah ya kawo min waraka. Na riski kaina ina tuhumar wanene ni? Kuma Allah ya jarrabceni da ƙishirwar amsar tambayata. Bana jin akwai wanda zai taimake ni a wannan lokacin bayan mahaliccina. Ba tare da zurfafa bayanai cikin abubuwan da na tsallake ba, ina son in tabbatarwa mai karatu cewa ni kam jeji shi yayi min maganin matsala ta. Ta hanyar komawa asali na, na fahimci kaina kuma na koyi yadda zan rayu da kaina, wannan ita ce waraka a gareni.
Duk abinda na sani, ko na koya, ko na ara na yafa a cikin wannan harka ta gado nayi shi ne kacokan don warkar da kaina, daga baya hakan ya zamto ganima a gareni. Wannan ganima ta zamto sanadin taimakon mutanen da ba zan iya kirga su ba a rayuwa. Adadin marasa lafiyan da na taimakawa ba zasu kirgu ba. Kuma har gobe ban daina ba.
Ina shawartar duk wanda yake da matsala ta depression da ya cire kunya ya je ya nemi taimako. Babban maganin depression yana jikin mai shi. Ka san kanka, idan ka san wanene kai to ko shedani saidai ya ganka ya kyale. Hakanan tattaunawa da mutanen da zasu fahimci matsalarka, ba tare da sun sa ka a mahangar rayuwarsu ba yana taimakawa matuka.
Ni kaina na taimakawa mutane da yawa sun tsallake wannan mataki kuma har yanzu ina yi. Watarana ina da burin ware wuri na musamman da lokacin don ganin irin wadannan marasa lafiyan.
Duk lokacin da aka ce mutum ya kasa rayuwa da kansa (inner self), to wannan mutum ya shiga depression. Kuma depression mugun yanayi ne da yake bukatar kulawa ta musamman.
Mutane da yawa suna fama da irin wannan matsalar amma basu da karfin guiwar da zasu faɗa har a taimaka musu ko su da kansu suyi wani yunkuri na taimakon kansu.
Yanayin depression shi kadai ne matsalar da makusantanka suke kokarin hana ka samu saukinsa ba da sanin su ba. Wadanda suke ganin suna son ka zasu shiga damuwa akan canjin dabi'a, muhalli da rayuwa da kake shiga sakamakon yunkurin magance matsalarka, kodayake ba da niyya suke hakan ba, amma yana da matukar tasiri wajen ƙara wa gishiri ciwo. Hakanan matsala ce da zaka dauki abubuwa da yawa a lokaci daya, zaka dauki kalubalen rashin jituwa tsakanin kanka da kanka (dabi'ar ka), sannan zaka fuskanci rashin jituwa tsakaninka da tsohuwar al'adar ka, muhallin ka, da sauransu.
A ka'ida, idan kana rashin lafiya ko makiyinka yana saurara maka yaga yadda Allah zai yi da kai, amma depression wanda yake saurara maka ma zai kawo wa zuciyarka farmaki.
Dalilai da yawa suna sa wannan ciwo, amma wanda ya fi karfi shine wanda za a jangwalo wani yanki (region) na zuciyarka, wanda ko kai kanka baka iya zuwa wajen. Kana iya jin ciwo idan ya taɓu, amma baka da ikon zuwa wajen ballantana ka sosa. Wannan yanki yafi komai gautsi a jikin mutum, kuma ido baya iya ganinsa, hannu baya iya taba shi, hanci baya iya riskar sansanonsa, a mutane kuwa, yan kadan ne Allah ya horewa ikon mallakar abinsu. Soyayya da kiyayya da dalilinsu suna iya tasiri wajen jangwalar wannan waje. Yarfe da dalilinsa, kazafi da dalilinsa, amana da cin amana da dalilinsu, alkawari da yaudara da dalilinsu, daukaka, nasara, gazawa da dalilinsu, kunci da yalwa da dalilinsu, arziki da talauci da dalilinsu, samu da rashi da dalilinsu duk wadannan suna daga cikin dalilan da ka jefa dan adam a cikin depression.
Allah yasa mu dace.
Mujahid Khalid,
Garkuwan Dawan Rano.
02/04/2023
Comments
Post a Comment