Posts

Showing posts from April, 2023

Tsokaci da shawarwari ga masu matsalar shafar Aljanu a mahangar al'ada ko likitancin zamani

Image
Gabatarwa A al'ada ta Hausawa, ana samun mutane masu larurar shafar aljanu, mutanen da aljanu suke sanyawa su fita daga ainihin hayyacinsu su shiga wani yanayi daban. Irin wadannan mutane suna sauya ɗabi'arsu da aka sansu da ita zuwa wata ɗabi'a daban. Misali, mutumin da bai jin turanci sai ya canza yare yana turanci kamar Bature, ko mai kunya ya koma mara kunya da sauransu. Irin wannan larura tana iya jawo matsaloli marasa adadi. Wasu daga cikin matsalolin suna canjawa daga lokaci zuwa lokaci, wasu kuma suna zaune a yanda suke. Baya ga sauyin dabi'a da majinyaci yake samu idan hakan ya faru da shi, ana iya samun wasu jinyoyi na zahiri da suke mamayar majinyacin a matsayin yan rakiya. Wadanna jinyoyi da suke zama yan rakiya, suna iya faruwa kafin majinyanci ya tsinci kansa a wannan yanayi ko bayan ya dawo hayyacinsa, misali, ciwon kirji, gazawar zuciya, ciwon ciki, ciwon mara, ciwon kai, ciwon kafa ko ciwon jiki gabadaya ka iya bijirowa a duk lokacin da alamomin babbar ...

SCHIZOPHRENIA DA LARURAR GANE-GANE (WADANDA ALJANU SUKE BUDEWA IDO)

Image
 Tun lokacin da na kalli wani wasan kwaikwayo da ake cewa Beautiful minds, wanda ya bi diddigin faman da wani masanin lissafi da ake cewa John Nash yayi da schizophrenia, hankali na ya karkata ga tunanin mecece wannan schizophrenia?  John Nash dan baiwa ne a fannin lissafi. Daga cikin irin gudunmawarsa da ba za a iya mantawa ba a lissafi ,John ya taimaka wajen yiwa mahangar Adam Smith kwaskwarima a fannin ilimin tattalin arziki, wannan aiki da John yayi ya taimaka wajen canja yadda ake koyar da ilimin tattalin arziki a duniya. A hakikanin gaskiya, wannan daya ne daga cikin gudummawoyi masu dimbin yawa da John ya samar a fannin lissafi. Saidai akwai abinda yake damun John, wata cuta da ake cewa Schizophrenia. Ko a cikin wannan wasan kwaikwayo, anyi tariya akan rayuwar da John yayi da abokin kwanansa a jami'a. Wannan abokin kwana na John shine babban abokinsa kuma abokin tattaunawarsa a fannoni daban daban da suka shafi akida, siyasa, soyayya da sauransu. Wannan abokin na John h...

SHAWARWARI GA MASU DEPRESSION

Image
Ko ƙarya ce in ka bata gaskiya watarana sai ta baka. Idan kana biɗar wani abu kar ka fasa. Idan masoyiya ce take biɗar masoyi, kar ta fasa, watarana zata samu abinda take so matukar ta bada gaskiya da amana ga abinda take. Na ga amfanin naci a gurare da yawa. Naga darasi akan mutane da dama. Lokacin da na fara harkar mu ta gado (harkar jeji), ranar farko da na shirya nace zan tafi farauta akwai wanda yace indai na iya zuwa ba zan iya dawowa ba. Na ɗauki gorar da kaka na yake riƙewa, nayi tafiyata. Haka muka je lafiya muka dawo lafiya. Idan na fito cikin unguwa, mutane suna kallona suna cewa 'Alabuda, alabuda, cau, cau, cau' da izgilanci. 🙂 Suna ganin wancan da yayi rayuwarsa a birni, dan boko, da girmansa yace zai yi farauta. Wasu suce shirme nake, zan daina, wasu su ce zan shiga hankali na gashinan dai. Amma da na bawa abin gaskiya, kuma na rike abinda nake da gaskiya da amana, sai Allah yasa min albarka a ciki. Ina iya tuna watarana ana wasan maƙera, sai nazo ina recording v...