Tsokaci da shawarwari ga masu matsalar shafar Aljanu a mahangar al'ada ko likitancin zamani
Gabatarwa A al'ada ta Hausawa, ana samun mutane masu larurar shafar aljanu, mutanen da aljanu suke sanyawa su fita daga ainihin hayyacinsu su shiga wani yanayi daban. Irin wadannan mutane suna sauya ɗabi'arsu da aka sansu da ita zuwa wata ɗabi'a daban. Misali, mutumin da bai jin turanci sai ya canza yare yana turanci kamar Bature, ko mai kunya ya koma mara kunya da sauransu. Irin wannan larura tana iya jawo matsaloli marasa adadi. Wasu daga cikin matsalolin suna canjawa daga lokaci zuwa lokaci, wasu kuma suna zaune a yanda suke. Baya ga sauyin dabi'a da majinyaci yake samu idan hakan ya faru da shi, ana iya samun wasu jinyoyi na zahiri da suke mamayar majinyacin a matsayin yan rakiya. Wadanna jinyoyi da suke zama yan rakiya, suna iya faruwa kafin majinyanci ya tsinci kansa a wannan yanayi ko bayan ya dawo hayyacinsa, misali, ciwon kirji, gazawar zuciya, ciwon ciki, ciwon mara, ciwon kai, ciwon kafa ko ciwon jiki gabadaya ka iya bijirowa a duk lokacin da alamomin babbar ...